Matsayin Sallah Da Hukuncinta Bayani Mece ce Sallah Ma’anar kalmar sallah a larabce Ita ce «Addu’a» Ma’anar Sallah a shari’ance Ita ce bautawa Allah da zantuka da ayyuka kevantattu, waxanda ake buxe su da kabbara, a rufe su da sallama. Matsayin Sallah A Musulunci 1 – Sallah ita ce rukuni na biyu a rukunan musulunci, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “An gina musulunci a bisa ginshiqai guda biyar, shaida wa babu abin bauta wa bisa cancanta sai Allah, kuma Muhammad bawansa ne Manzonsa ne, da tsayar da sallah…..” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] . 2 – Sallah ita ce mafi falalar ayyuka, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Mafi falalar ayyuka sallah a farkon lokacinta” [ Tirmizi ne ya rawaito shi] . 3 – Sallah ce mararraba tsakanin musulunci da kafirci, Annabi (S.A.W) ya ce, “Haqiqa tsakanin mutum da shirka da kafirci barin sallah” [Muslim ne ya rawaito shi] . 4 – Sallah ita ce ginshiqin musulunci, a kanta ne – bayan tauhidi – aka gina musulunci, Annabi yana cewa “Kan wannan ...