Skip to main content

Matsayin Sallah Da Hukuncinta BY MUSA MUHAMMAD MUKTAR

Matsayin Sallah Da Hukuncinta
Bayani Mece ce Sallah
Ma’anar kalmar sallah a larabce
Ita ce «Addu’a»
Ma’anar Sallah a shari’ance
Ita ce bautawa Allah da zantuka da ayyuka kevantattu, waxanda ake buxe su da kabbara, a rufe su da sallama.
Matsayin Sallah A Musulunci
1 – Sallah ita ce rukuni na biyu a rukunan musulunci,
Manzon Allah (S.A.W) ya ce,
“An gina musulunci a bisa ginshiqai guda biyar, shaida wa babu abin bauta wa bisa cancanta sai Allah, kuma Muhammad bawansa ne Manzonsa ne, da tsayar da sallah…..” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] .
2 – Sallah ita ce mafi falalar ayyuka,
Manzon Allah (S.A.W) ya ce,
“Mafi falalar ayyuka sallah a farkon lokacinta” [ Tirmizi ne ya rawaito shi] .
3 – Sallah ce mararraba tsakanin musulunci da kafirci,
Annabi (S.A.W) ya ce,
“Haqiqa tsakanin mutum da shirka da kafirci barin sallah”
[Muslim ne ya rawaito shi] .
4 – Sallah ita ce ginshiqin musulunci, a kanta ne – bayan tauhidi – aka gina musulunci,
Annabi yana cewa “Kan wannan lamari gabaxaya shi ne musulunci, ginshiqinsa kuwa sallah” [Ahmad ne ya rawaito shi]
Falalar Sallah
1 – Sallah haske ce ga ma’abocinta, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Sallah haske ce” [Muslim ne ya rawaito shi] .
2 – Sallah kaffara ce daga zunubai, Allah Maxaukakin sarki ya ce, “Ka tsaida sallah a gefen rana da wani yanki a cikin dare, haqiqa kyawawan ayyuka suna tafiyar da munana, wannan tunatarwa ce ga masu tunawa” . (Hud: 114) .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce,
“Ku bani labari da ace akwai qorama a qofar xayanku, yana wanka a cikinta a kowace rana sau biyar, shin wani abu zai ragu na dattinsa, sai suka ce “Babu wani dattinsa da zai ragu” sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Hakanan misalin salloli biyar suke, Allah yana goge zunubai da su” [Bukhari ne da Muslim ne suka rawaito shi] .
3 – Sallah sababin shiga Aljannah ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce wa Rabi’a xan Ka’abu – yayin da ya roqe shi zama tare da shi a Aljannah – sai Manzon Allah ya ce masa
“Ka taimaka mi a kan kanka da yawan sujjada (Watau sallah)”
[ Muslim ne ya rawaito shi] .
Hukuncin Sallah
Salloli guda biyar xin nan wajibi ne da Alqur’ani da Sunnah da Ijma’i.
1 – Dalili daga Alqur’ani :
Allah ya ce, “Ku tsayar da Sallah ku bada zakkah, ku yi ruku’u tare da masu ruku’u” (Albaqra : 43) .
2 – Dalili daga sunnah :
Manzon Allah (S.A.W) ya ce,
“An gina musulunci a kan ginshiqai biyar : Shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah, Kuma Muhammad Bawansa ne Manzonsa ne, da tsayar da sallah, da bayar da zakkah, da ziyartar xakin Allah, (Hajji) da azumin Ramadan”
[Bukhari ne da Muslim ne suka rawaito shi] .
- An karvo daga Xalhatu xan Ubaidillahi, ya ce, wani mutum ya tambayi Annabi (S.A.W) game da musulunci, Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Salloli biyar a cikin yini da dare” Sai ya ce, “Shin akwai wasu daban a kaina ban da su?” Sai Manzon Allah ya ce, “A’a, sai dai ka yi nafila” [ Bukhari ne da Muslim ne suka rawaito shi] .
3 – Dalili daga Ijma’i :
Al’umma gabaxayanta ta haxu a kan wajabcin salloli biyar a cikin yini da dare.
Su Waye Sallah Ta Wajaba A Kansu?
Sallah ta wajaba a kan dukkan musulmi, baligi, namiji ko mace.
Hukuncin Wanda Baya Sallah
1 – Wanda Ba Ya Sallah, Kuma Yana Inkarin Wajabcinta :
A sanar da shi idan bai sani ba, idan ya ci gaba da inkarinta to shi kafiri ne, mai qaryata Allah da Manzonsa da haxuwar Musulmai.
2 – Wanda Ba Ya Sallah Saboda Kasala :
Wanda ya bar sallah da gangan saboda kasala ya kafirta, wajibi ne akan shugaba ya kira shi zuwa ga yin sallah, ya bijirar masa da tuba, har tsawon kwana uku, idan ya tuba shike nan, in kuwa bai tuba ba, shugaba ya kashe shi a matsayin kafiri wanda ya yi ridda, saboda faxin Manzon Allah (S.A.W) “Alqawarin da yake tsakaninmu da su shi ne sallah, duk wanda ya bar ta haqiqa ya kafirta” [Tirmizi ne ya rawaito shi] .
Da faxinsa (S.A.W) “Tsakanin mutum da shirka da kafirci shi ne barin sallah” [Muslim ne ya rawaito shi] .  

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU. Daga Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano.Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai 'siffatul ijza' (ta wadatar), kuma wacce ake kira 'siffatu kamal' (ta kamala).Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da zaka fara yi shi ne:zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka ، a dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana kayi tsarki kenan، to daga nan kuma sai kayialwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah zakayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shiba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyua cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya ...

NASIHA AKAN WANDA BAYA SALLAH KO YAKE WASA DA ITA BY MUSA MUHAMMAD MUKTAR

Tsoratarwa Akan Wanda Ba Ya Yin Sallah Ko Yake Wasa Da Ita Tsoratarwa Akan Wanda Ba Ya Yin Sallah Ko Yake Wasa Da Ita Sallah daya ce daga cikin rukunnan musulinci guda biyar wanda musuluncin bawa ba ya cika har ya tsayar da ita. Mazon Allah SAW yana cewa: "Tsakanin mutum da tsakanin shirka da kafirci, shine barin Sallah. (Muslim). Manzon Allah SAW yana cewa: "Alkawarin da yake tsakanin mu da kafurai ita ce sallah, dukkan wanda ya bar sallah to ya kafirta). @ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ ﻭﻏﻴﺮﻩ . Imam Tirmizy ya ruwaito daga Abdillahi bn Shaqeeq al'ukaily yace: "Sahabban Annabi Muhammad s.a.w basu ganin barin aiki wani aiki kafircine inbanda sallah". @ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ. Wato sun hadu akan dukkan wanda ya bar sallah kafiri ne. Manzon Allah s.a.w yana cewa: "Farkon abinda za'ayi wa bawa hisabi akansa na aiyukansa shine sallah, idan ta cika ta yi kyau ya tsira kuma ya rabauta, idan ba ta yi kyau ba kuma bata cika ba ya halaka ya tabe, idan an sami nakasa a cikin f...

029- SUJJADAR RAFKANNUWA (KABALIYYAH DA BA’ADIYYAH) ›

Gabatarwa: Ayanzu da izinin Allah muna son mu kawo bayanaine da suka shafi sujjar rafkannuwa wacce ake kira Kabaliyyah ko ba’adiyya da fatan Allah ya anfanar da mu da wadannan bayanai, kuma ya sanya ya zama sanadiyyar tsira duniya da lahira. Wadannan bayanai za su kunshi me ake nufi da sujjadar rafkannuwa ko mecece kabaliyyah sannan mecece ba’adiyyah, sannan a kawo bayanai na abinda ke sabbaba wadannan sujjadu. Sujjadar Rafkannuwa: Sujjadune guda biyu da mutum yake yinsu bayan ya kammala sallah kafin sallama ko bayan sallama saboda kari ko ragi ko kokwanto da ya yi a cikin sallah. Wannan ta’arifi da ya gabata ya fayyace mana me ake nufi da sujjadar rafkannuwa kuma ya yi bayanin abinda yasa ake yenta da kuma lokacin da ake yenta da kuma dadi nawa ake yi. Kabaliyyah : Sune sujjadu biyu da ake yi bayan tahiyyah kafin sallama, kasancewa ana yinta kafin sallama shi yasa ake kiranta kabaliyyah wato ‘Kabals Salam’. Ba’adiyyah: Sune sujjadu biyu da ake yi bayan an sallame daga sallah, sa...