Skip to main content

NASIHA AKAN WANDA BAYA SALLAH KO YAKE WASA DA ITA BY MUSA MUHAMMAD MUKTAR

Tsoratarwa Akan Wanda Ba Ya Yin Sallah Ko Yake Wasa Da Ita

Tsoratarwa Akan Wanda Ba Ya Yin Sallah Ko Yake Wasa Da Ita
Sallah daya ce daga cikin rukunnan musulinci guda biyar wanda musuluncin bawa ba ya cika har ya tsayar da ita.
Mazon Allah SAW yana cewa:
"Tsakanin mutum da tsakanin shirka da kafirci, shine barin Sallah. (Muslim).
Manzon Allah SAW yana cewa:
"Alkawarin da yake tsakanin mu da kafurai ita ce sallah, dukkan wanda ya bar sallah to ya kafirta).
@ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ ﻭﻏﻴﺮﻩ .
Imam Tirmizy ya ruwaito daga Abdillahi bn Shaqeeq al'ukaily yace:
"Sahabban Annabi Muhammad s.a.w basu ganin barin aiki wani aiki kafircine inbanda sallah".
@ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ.
Wato sun hadu akan dukkan wanda ya bar sallah kafiri ne.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
"Farkon abinda za'ayi wa bawa hisabi akansa na aiyukansa shine sallah, idan ta cika ta yi kyau ya tsira kuma ya rabauta, idan ba ta yi kyau ba kuma bata cika ba ya halaka ya tabe, idan an sami nakasa a cikin farilla, sai Allah ya ce: ku yi dubi shin bawana yana sallolin nafila, sai ku cike gurbin farillah da ita, sannan sauran aiyuka su kasance kamar haka".
@ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ ﺃﻳﻀﺎ ﻭﻏﻴﺮﻩ .
Annabi s.a.w yana cewa:
"Farkon abinda za'a fara yi wa bawa hisabi akan sa na aiyukansa ranar alkiyama ita ce Sallah, idan ta yi kyau to sauran aiyukansa ma sunyi kyau, idan ta baci sauran aiyukansa ma sun baci".
@ ﻭﺭﻭﻯ ﺍﻟﻄّﺒﺮﺍﻧﻲ .
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
"Wanda ya kiyaye Sallah yana da haske da hujja da tsira a gobe alkiyama, wanda kuma bai kiyaye sallah ba, ba ya da haske da hujja da tsira, a ranar alkiyama yana tare da Karuna da Hamana da Fir'auna da Ubaiyu bn Khalaf".
@ ﻭﺭﻭﻯ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﻏﻴﺮﻩ .
HUKUNCIN WANDA BA YA SALLAH.
Wadanda ba sa yin sallah nau'i biyu ne:
1-Nafarko
"Wanda ya bar yin sallah da gangan tare da kin yarda akan wajibcin sallah, wato ba ya yin sallah kuma yana ganin yin sallah ba wajibi bane, to wannan kafiri ne a bisa haduwar dukkan musulmai baki daya, kuma kafircin da yake fitar da shi daga musulinci gaba daya".
¤ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
Yana cewa:
"Babu sabani a tsakanin malamai cewar wanda ya bar yin sallar farillah da gangam,yana cikin mafi girman zunubi kuma laifine daga cikin manyan laifuka wanda yafi laifin kisan kai da fashi da makami,yafi laifin zina da da shan giya da dukkan wani laifi, kuma sakamakonsa shine halaka da tabewa da masifa tun daga nan duniya har zuwa lahira".
2-Na biyu
"Wanda ba ya yin Sallah saboda kasala da ha'inci, wani lokacin ya yi wani lokacin ya ki yi, amma tare da yardar cewa yin sallar wajibi ne, wannan shine yana cikin laifi mai girma kuma yana cikin alamar munafinci babba, mai wannan halin za a yi masa nasiha da wa'azi cikin hikima.....".
Malamai sun kasu kashi uku akan mai wanann halin;-
i-Imam Malik da Shafi'i da Imam Ahmad awata riwaya daga wajansa,sun hadu akan cewa:
"Mai wannan aikin ba kafiri bane amma yana cikin fasiqai za'a nemi ya tuba,idan ya tuba to idan kuma bai tubaba za'a kasheshi a matsayin Haddi da takobi".
ii-Wasu daga cikin magabata sun tafi kaman yana zaman kafiri,wannan itace dayar riwayar Imam Ahmad da wasu daga cikin malaman Shafi'yya.
iii-Amma Imam Abu Hanifa ya tafi akan wanda baya sallah dan kasala da ha'inci tare da yarda da wajibancin Allah, cewa:
"Ba ya zaman kafiri kuma ba za a kashe shi ba sai dai za'a matsa masa har sai ya yi Sallar".
Allah ne mafi sani.
Allah ka bamu ikon tabbatuwa akan yin sallah akan lokacinta kuma cikakkiya irinta Annabi SAW har zuwa mutuwarmu.

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU. Daga Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano.Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai 'siffatul ijza' (ta wadatar), kuma wacce ake kira 'siffatu kamal' (ta kamala).Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da zaka fara yi shi ne:zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka ، a dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana kayi tsarki kenan، to daga nan kuma sai kayialwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah zakayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shiba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyua cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya ...

029- SUJJADAR RAFKANNUWA (KABALIYYAH DA BA’ADIYYAH) ›

Gabatarwa: Ayanzu da izinin Allah muna son mu kawo bayanaine da suka shafi sujjar rafkannuwa wacce ake kira Kabaliyyah ko ba’adiyya da fatan Allah ya anfanar da mu da wadannan bayanai, kuma ya sanya ya zama sanadiyyar tsira duniya da lahira. Wadannan bayanai za su kunshi me ake nufi da sujjadar rafkannuwa ko mecece kabaliyyah sannan mecece ba’adiyyah, sannan a kawo bayanai na abinda ke sabbaba wadannan sujjadu. Sujjadar Rafkannuwa: Sujjadune guda biyu da mutum yake yinsu bayan ya kammala sallah kafin sallama ko bayan sallama saboda kari ko ragi ko kokwanto da ya yi a cikin sallah. Wannan ta’arifi da ya gabata ya fayyace mana me ake nufi da sujjadar rafkannuwa kuma ya yi bayanin abinda yasa ake yenta da kuma lokacin da ake yenta da kuma dadi nawa ake yi. Kabaliyyah : Sune sujjadu biyu da ake yi bayan tahiyyah kafin sallama, kasancewa ana yinta kafin sallama shi yasa ake kiranta kabaliyyah wato ‘Kabals Salam’. Ba’adiyyah: Sune sujjadu biyu da ake yi bayan an sallame daga sallah, sa...