Skip to main content

HUDUBAR JUMU' A DAGA MASALLACIN JUMU' A NA IHYA ' US SUNNAH DAKE KOFAR NASSARAWA KANO AUDIO MP 3 ( Basheer Journalist Sharfadi )

HUDUBAR JUMU' A DAGA MASALLACIN JUMU' A NA IHYA ' US SUNNAH DAKE KOFAR NASSARAWA KANO AUDIO MP 3 ( Basheer Journalist Sharfadi )

-A yau Jumu'a 21/Shawwal/1436. Wadda tayi dai-dai da 07/Aug/2015. Babban Limamin Masallacin Jumu'a na Ihya'us-Sunnah dake Kofar Nassarawa a Karamar Hukumar Birnin Kano da Kewaye. Sheik Dr. Muhammad Sani Ashir Kano Shine Ya Jagoranci Huduba da Sallah a Masallacin.
-Dr. Sani Ashir Kano ya fara gabatar da Hudubar sa ne da misalin Karfe 12:30 na rana a Masallacin. Inda aka tayar da Sallah da Karfe 01:05 na rana Bayan Kammala Hudubar. Babban Limamin Yayi Hudubar ne Akan Tauhidi wato Kadaita Allah da yi masa bauta shi kadai.
-An gudanar da Sallar cikin nutsuwa da kwanciyar Hankali Kamar Yadda aka saba tare da Gudummuwar Yan agaji wajen bayar da da kyakykyawar Kulawa Domin ganin ayyuka sun gudana kamar yadda aka saba.
-Kar dai na cikaku da surutu Danna Kasa Domin Sauraron Hudubar daga Bakin Dr.:


Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU. Daga Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano.Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai 'siffatul ijza' (ta wadatar), kuma wacce ake kira 'siffatu kamal' (ta kamala).Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da zaka fara yi shi ne:zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka ، a dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana kayi tsarki kenan، to daga nan kuma sai kayialwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah zakayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shiba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyua cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya ...

NASIHA AKAN WANDA BAYA SALLAH KO YAKE WASA DA ITA BY MUSA MUHAMMAD MUKTAR

Tsoratarwa Akan Wanda Ba Ya Yin Sallah Ko Yake Wasa Da Ita Tsoratarwa Akan Wanda Ba Ya Yin Sallah Ko Yake Wasa Da Ita Sallah daya ce daga cikin rukunnan musulinci guda biyar wanda musuluncin bawa ba ya cika har ya tsayar da ita. Mazon Allah SAW yana cewa: "Tsakanin mutum da tsakanin shirka da kafirci, shine barin Sallah. (Muslim). Manzon Allah SAW yana cewa: "Alkawarin da yake tsakanin mu da kafurai ita ce sallah, dukkan wanda ya bar sallah to ya kafirta). @ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ ﻭﻏﻴﺮﻩ . Imam Tirmizy ya ruwaito daga Abdillahi bn Shaqeeq al'ukaily yace: "Sahabban Annabi Muhammad s.a.w basu ganin barin aiki wani aiki kafircine inbanda sallah". @ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ. Wato sun hadu akan dukkan wanda ya bar sallah kafiri ne. Manzon Allah s.a.w yana cewa: "Farkon abinda za'ayi wa bawa hisabi akansa na aiyukansa shine sallah, idan ta cika ta yi kyau ya tsira kuma ya rabauta, idan ba ta yi kyau ba kuma bata cika ba ya halaka ya tabe, idan an sami nakasa a cikin f...

025- SUNNONIN SALLAH

025- SUNNONIN SALLAH Shinfida: Su sunnonin sallah su ne ke biye da farillan sallah wurin matsayi a cikin sallah, saboda haka kamar yadda bai kamata ka yi wasa da farillan sallah ba to haka yake bai kamata ka yi wasa da sunnonin sallah ba. Wasu da zarar sun ji ance abu kaza sunna ne to basa daukan shi da girma domin suna ganin rashin sa ba zai hana musu sallah ba, alhali kuwa wannan kuskurene mai girman gaske, ai ko ba’a sallah ba duk abinda ka ji an ce sunnane to bai kamata ka yi wasa da shiba. Su wadannan sunnoni na sallah kamar yadda bayani ya gabata matsayinsu baikai na farilla ba domin idan ka bar farilla daya a raka’a sai dai ka ajiye wannan raka’ar ka kawo wata makwafinta kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah a lokacin bayani kan kabaliyyah da ba’adiyya. Kennan su sunnonin sallah ba haka bane, idan mutum ya cika su to sallar shit a cika, idan ko bai cika su ba to sallar shi bata cika ba ko da ko ba zai sake ta ba. Saidai su sunnonin sallah asune ake samun damar kyara...