Shinfida: Su wadanann abubuwa su malamai suke kira ‘Makruhatus Salah’ wato abubuwan da ba’a so ayi su a cikin sallah, domin yinsu yana matukar ragewa mutum ladan sallarsa, dudda sallar bat abaci ba ta yadda za’a ce sai ya sake, kuma ba zai yi kabaliyyah ko ba’adiyyah saboda ya yisu ba, saboda haka sai a kiyaye kada mutum ya yi wasa da sallarsa, Hssan dan Atiyyah yake cew: ‘’Lalle mutane biyu za su iya kasancewa a cikin sallah guda, amma tazarar dake tsakaninsu na falala ya fi nisan sama da kasa’’. Lalle wannan ba karamar Magana bace indai har mutane biyu za su kasance a sallah guda bayan limami guda amma banbancin dake tsakaninsu ya dara tazarar dake tsakanin sama da kasa, to kan lalle bakaramin banbanci bane, sannan tambaya anan itace: Me ya janyo wannan banbanci na falala?. Natsuwa kwantar da hankali kankar-da-kai, da kuma sanin me mutum yake yi da nisantar abinda ba’a so mutum ya yi a cikin sallah, wadannan kadanne daga cikin abubuwan da za su banbanta falalar masallata, ga kadan...