Skip to main content

027- ABUBUWAN DA BA’A YIN SU A SALLAH

Shinfida: Su wadanann abubuwa su malamai suke kira ‘Makruhatus Salah’ wato abubuwan da ba’a so ayi su a cikin sallah, domin yinsu yana matukar ragewa mutum ladan sallarsa, dudda sallar bat abaci ba ta yadda za’a ce sai ya sake, kuma ba zai yi kabaliyyah ko ba’adiyyah saboda ya yisu ba, saboda haka sai a kiyaye kada mutum ya yi wasa da sallarsa, Hssan dan Atiyyah yake cew: ‘’Lalle mutane biyu za su iya kasancewa a cikin sallah guda, amma tazarar dake tsakaninsu na falala ya fi nisan sama da kasa’’.
Lalle wannan ba karamar Magana bace indai har mutane biyu za su kasance a sallah guda bayan limami guda amma banbancin dake tsakaninsu ya dara tazarar dake tsakanin sama da kasa, to kan lalle bakaramin banbanci bane, sannan tambaya anan itace: Me ya janyo wannan banbanci na falala?.
Natsuwa kwantar da hankali kankar-da-kai, da kuma sanin me mutum yake yi da nisantar abinda ba’a so mutum ya yi a cikin sallah, wadannan kadanne daga cikin abubuwan da za su banbanta falalar masallata, ga kadan daga cikin abubuwan da ba’a so a yi su a cikin sallah:
1.Waiwaye: Shi waiwaye ya kasu kasha buyu; Kashi na farko shine ‘waiwayen zuciya’ wato zuciyar mai sallah ta kasance ba anan take ba ta kada ta yi wani wuri, wannan nau’i na waiwaye yana matukar rage ladan sallah, saboda haka kullum sai ka yi kokarin hana zuciyarka tafiya wani wuri lokacin sallah. Waiwaye na biyu shine ‘waiwayen jiki’ wato mutum ya tunga waige yana sallah, ya waiga dama ya kuma waiga hagu, wani lokcimma ya daga kai sama, Allah ya sawwake.
2. Rufe Ido: Ida nana sallah bude idanuwa ake yi ba’a rufesu domin rufe idanuwa ba’a ibada dashi a musulunci.
3. Tsayawa Akan Kafa Guda: Wani ida yana sallah sai ya bada karfinsa akan kafarshi guda, wani ya dauki kafar ya dorata akan dayar, wannan ba’a son shi a cikin sallah. Saidai malamai sukace idan tsayuwarce ta yi tsawo to wannan ba komai.
4. Hada Kafafuwa: Wasu idan suna sallah sai su hada kafafuwansu maimakon su ware su, wannan hada kafafuwa da suke yi kuskurene a sallah, saboda haka kullum a dinga kusantar malamai domin sanin hukunce-hukuncen sallar nan.
5. Tunani Akan Duniya: Abinda ake so idan kana sallah ka dainga tunani kan ayoyin da kake karantawa a sallar ko limaminku yake karantawa. Wannan zai sa ba zaka shiga cikin tunanin duniyaba, kada ka manta shaidan a koda yaushe so yake ya samu rabonsa a ibadarka, domin kuwa wani tunanin bai zuwa maka sai ka fara sallah, saboda haka kai kuma ka nemi taimakon Allah akan ba zaka bashi wannan damarba.
6. Kin Kashe Waya: Kin kashe waya yana cikin abubuwan da suke ragewa mutum ladan sallar shi, domin ta yi kararnan tana dauke hankalinka da na liman da na sauran masallata ashe bakaramin hatsari bane kin kashe waya a lokacin sallah. Abinda ake so anan shine da zarar ka kama hanyar masallaci ana rubuta maka ladane saboda haka sai ka kashe wayarka ka fara tanadarwa kanka natsuwa, koda kana cikin sallah sai ka tuna baka kashe wayarkaba ya halatta ka cirota ka kashe, ko ka ji an kira wani, shi yasa malamai sukace ‘’Da nisantar dukkan abinda zai shagaltar das hi daga barin anboton Allah’’ . Wato ya bar duk abinda zai hana mishi wannan.
7. Kaya A Aljihu: Hakanan ba’a bukatar mutum ya zuba kaya a cikin aljihunsa wanda zai iya daukar hankalinsa ya shagaltar da shi, wani sai ya cika aljihunshi da mangwaro ko lemo ko wayoyi ko mabudan kofa, abinda ake Magana akai shi fa masallaci yana gaban Ubangijine saboda haka ake bukatar ya samu cikakkiyar natsuwa.
8. Motsa Yatsu: Shi kuma wani yana sallah yana motsa yatsunsa sunawa; kas,kas, wani kuma yana ta wasa da gemu ko a gogo ko ya cire hula, wani kuma hannunsa yake sawa a kugunsa, wanda yake kamar yadda bayanai suka gabata shaidan yana son sai ya rage maka ladan sallarka ne.
9. Bayan An Kawo Abinci: Hakanan an fi so ka ci abinci idan har an kawoshi kafin ka fara sallah musamman idan kana matukar son ka ci abincin, amma wannan bas hi ke nuna cewa ‘Ci na gaba da sallah ba’.
10. Ware Wani Abu Domin Yin Sujjada Akan Shi: Kuma ba’a so mutum ya ware wani abu ya zama akan shi zai dinga yin sujjada domin yin haka koyine da masu bin addinin Shi’a, kuma ba’a yarda kai ka yi ko yi da su ba.
11. Share Hannu Ko Hanci: Ba’a so ba aduk lokacin da ka yi sujjada ace sai ka share hannuwanka da kuma hancinka a lokacin da kake cikin sallah, amma idan bayan ka idar da sallar ne to wannan ba komai.
12. Inda Yake Da Hotuna: Hakanan an kyamaci ka yi sallah a inda yake da hotuna an manna su a bangone ko an jingine su ne, domin hakan ko yi ne da masu bautar gumaka, kuma ko yi ne da Nasara.
13. Shinfida Hannu: Kuma ba’a so a lokacin da kake sujjada kamar yadda kare yake shinfida hannuwansa, abinda ake so shine ka shinfida tafukan hannuwanka.
14. Rashin Natsuwa: Ba’a so mutum ya fara sallah alhalin bai natsuba, saboda haka kada ya fara sallah yana mai matse tusa, ko fitsari ko bayangida ko kuma matsanancin kishin ruwa da matsananciyar yunwa.
Kammalawa: Wadannan bayanai sun nuna mana cewa lalle mu tashi tsaye domin cire rabon shaidan daga cikin ibadarmu, Allah Ya taimaka mana.

Post by IRSHAD group of school islamiyya students

1. Musa Muhammad Muktar
2.Mustapha Danjuma
3. Haruna Muhammad
4. Muhammad Auwal
5. Muktar Usman
6. Fadeela Abdulkareem
7. Munira Muhammad
8. Haleemah Umar

Fo  booking call Malama ummi 08065771988

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU. Daga Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano.Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai 'siffatul ijza' (ta wadatar), kuma wacce ake kira 'siffatu kamal' (ta kamala).Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da zaka fara yi shi ne:zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka ، a dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana kayi tsarki kenan، to daga nan kuma sai kayialwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah zakayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shiba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyua cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya ...

NASIHA AKAN WANDA BAYA SALLAH KO YAKE WASA DA ITA BY MUSA MUHAMMAD MUKTAR

Tsoratarwa Akan Wanda Ba Ya Yin Sallah Ko Yake Wasa Da Ita Tsoratarwa Akan Wanda Ba Ya Yin Sallah Ko Yake Wasa Da Ita Sallah daya ce daga cikin rukunnan musulinci guda biyar wanda musuluncin bawa ba ya cika har ya tsayar da ita. Mazon Allah SAW yana cewa: "Tsakanin mutum da tsakanin shirka da kafirci, shine barin Sallah. (Muslim). Manzon Allah SAW yana cewa: "Alkawarin da yake tsakanin mu da kafurai ita ce sallah, dukkan wanda ya bar sallah to ya kafirta). @ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ ﻭﻏﻴﺮﻩ . Imam Tirmizy ya ruwaito daga Abdillahi bn Shaqeeq al'ukaily yace: "Sahabban Annabi Muhammad s.a.w basu ganin barin aiki wani aiki kafircine inbanda sallah". @ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ. Wato sun hadu akan dukkan wanda ya bar sallah kafiri ne. Manzon Allah s.a.w yana cewa: "Farkon abinda za'ayi wa bawa hisabi akansa na aiyukansa shine sallah, idan ta cika ta yi kyau ya tsira kuma ya rabauta, idan ba ta yi kyau ba kuma bata cika ba ya halaka ya tabe, idan an sami nakasa a cikin f...

025- SUNNONIN SALLAH

025- SUNNONIN SALLAH Shinfida: Su sunnonin sallah su ne ke biye da farillan sallah wurin matsayi a cikin sallah, saboda haka kamar yadda bai kamata ka yi wasa da farillan sallah ba to haka yake bai kamata ka yi wasa da sunnonin sallah ba. Wasu da zarar sun ji ance abu kaza sunna ne to basa daukan shi da girma domin suna ganin rashin sa ba zai hana musu sallah ba, alhali kuwa wannan kuskurene mai girman gaske, ai ko ba’a sallah ba duk abinda ka ji an ce sunnane to bai kamata ka yi wasa da shiba. Su wadannan sunnoni na sallah kamar yadda bayani ya gabata matsayinsu baikai na farilla ba domin idan ka bar farilla daya a raka’a sai dai ka ajiye wannan raka’ar ka kawo wata makwafinta kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah a lokacin bayani kan kabaliyyah da ba’adiyya. Kennan su sunnonin sallah ba haka bane, idan mutum ya cika su to sallar shit a cika, idan ko bai cika su ba to sallar shi bata cika ba ko da ko ba zai sake ta ba. Saidai su sunnonin sallah asune ake samun damar kyara...