Skip to main content

032. ABUBUWAN DA SUKE KAWO BA’ADIYYAH (2)

Gabatarwa: wannan shine tsagi na biyu na abubuwan da suke janyo ba’adiyyah a cikin sallah, ta fatan zamu kara kusantar malamai.
Kokwanto:
Idan mutum ya yi kokwanton sallarshi ta cika ko bata cika ba sai ya kawo abinda ya yi kokwanton sannan ba’adiyyah, misali; Idan ya yi kokwanton shin ya yi sujjadar ta cika ko bata cika ba, sai ka cika sannan ka yi ba’adiyyah.
Idan mutum ya yi kokwanton wannan raka’ar itace ta hudu ko itace ta uku sai ya barta itace tau kun sai ya kawo cikon ta hudun sannan ya yi ba’adiyyah.
Mutum mai yawan wasuwasi to abinda da ake so daga gareshi shine yabar wasuwasin ya kakkabeshi daga zuciyarsa ba zai kawo abinda ya yi kokwanton akanshi ba, sai bayan ya sallame sai ya yi ba’adiyyah, shin kokwanton akan karine ko akan ragi. Wannan yana nuna mana mafita daga mutanan da suke da yawan kokwanto da wasuwasi, Allah ya yaye musu mu kuma ya tsaremu, amin.
Idan mutum ya yi shakkun yana da hadasi ko bai da shi? Sannan sai ya dan yi tunani kadan sai kuma ya samu tabbas akan yana da tsarki to ba komai akanshi, dudda ya yi hakan ne a cikin sallah.
Yin rafkannuwa a sallolin da ake ramakwansu daidaine da wadanda ake yin su cikin lokaci ba banbanci, kenan suma kabaliyyah da ba’adiyyah tana shiga cikinsu.
 Idan mamu ya yi lafkannuwa alokacin yana bayan liman to liman ya dauke masa, misali; da aka yi zaman tahiya na farko kawai sai ka yi sallama ka dauka an gama sallar, ko kuma kuna sujjada sai ka ji wani ya yi kabbara sai ka taso daga sujjadar ka dauka liman sai ka ga ba haka bane sai ka koma sujjadar duk bakomai akanka, saboda kana bayan liman.
Idan masabuki (wanda yake ciko sallarsa bayan sallamar liman) ya yi rafkannuwa a lokacin da yake kawo raka’o’in da suka wuce masa bayan sallamar liman to fa anan hukuncinsa hukuncin mai sallah ne shi kadai saboda haka ba’abinda liman ya dauke masa domin tuni liman ya sallame shi, saboda haka idan kabaliyyah ta kamashi a wannan lokacin sai ya yi ta hakama idan ba’adiyyah ce.
Idan kabaliyyah ko ba’adiyyah ta kama liman to ta shafi mamu ko tare dashi abin ya faru ko ba tare da shi bane.
Idan kabaliyyah ta kamaliman to mamu zai yi tare da liman, sannan idan liman ya sallame sai ya mike ya kawo ragowar raka’o’insa. Amma idan ba’adiyyah ce to bazaka yi tare da liman ba har sai ka ciko ragowar abinda ake binka ka yi sallama sannan ka yi ta, kasan dalilin da liman ya yi ta ko baka saniba.
Idan mutum ba’adiyyah ta kamashi ta bangaran liman, sannan da ya tashi yana kawo abinda ya saura akansa sai kuma kabalillah ta same shi to anan idan ya yi kabaliyyar ta wadatar, ba sai ya yi ba’adiyyar ba.
Wanda ya yi kokwanton ‘‘shin yanzu yana wuturine ko yana raka’a ta biyun shafa’ine’’? to sai ya barta itace raka’a ta biyun shafa’in, sannan bayan ya sallame sai ya yi ba’adiyyah sai kuma ya mike ya kawo wuturin.
Idan kuna sallah tare da liman sai shi limamin ya yi rafkannuwa ta yadda ya yi kari ko ya rage to mamu tasbihi zai yi, sai kace ‘’Subhanallahi’ ’, idan liman ya kara sujjada ta zama uku to abinda zaka yi shine tasbihi ba zaka yi sujjadar ta uku tare da shi ba.
Idan liman ya tashi zuwa raka’a ta biyar to duk wanda ya tabbatar itace ta hudun sai ya bishi, haka kuma duk wanda yake kokwanto; shin ta biyarce ko ta hudu, to shima zai mike ya bishi. Amma duk wanda ya tabbatar wannan raka’ar itace ta biyar to ba zai bi shi ba sai ya yi zamanshi.
Idan liman ya sallame kafin sallah ta cika, to wadanda ke bayansa sai su yi masa tasbihi wato su ce
‘’Subhanallah’’ , idan liman ya gasgata wanda ya yi tasbihin sai ya mike ya ciko sallar, sai kuma a yi ba’adiyyah, idan kuwa liman yana kokwanto akan hakan, sai ya tambayi mutane biyu adilai, kuma ya halatta su yi Magana anan, idan kuwa shi liman yanada yakini akan sallar ta cika to sai ya yi aiki da yakinin na sa, ya ajiye tanbayar, saidai idan mutanen dake bayansa sun ta tasbihi sai ya bar yakinin na sa, ya koma zuwa ga abinda suke a kai, kamar yadda mai Akhdari ya zayyano.
Kammalawa: Wannan shine gwargwadon abinda ya samu na bayani akan rafkannuwa a cikin salloli na farilla, ko na ramuwa ko wadanda ake yin su a lokacinsu, da fatan zamu kara kusantar inda malamai suke. Akaro na gaba da izinin Allah madaukakin Sarki zamu kawo bayanaine dangane da rafkannuwa a cikin salloli na nafilfili. Ga dukkan mai tambaya kofa a bude take, fatammu shine Allah ya karbi ayyukammu ya kuma sanya mu cikin wadanda ya yiwa rahama.

Post by IRSHAD group of school islamiyya students

1. Musa Muhammad Muktar
2.Mustapha Danjuma
3. Haruna Muhammad
4. Muhammad Auwal
5. Muktar Usman
6. Fadeela Abdulkareem
7. Munira Muhammad
8. Haleemah Umar

Fo  booking call Malama ummi 08065771988

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU. Daga Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano.Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai 'siffatul ijza' (ta wadatar), kuma wacce ake kira 'siffatu kamal' (ta kamala).Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da zaka fara yi shi ne:zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka ، a dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana kayi tsarki kenan، to daga nan kuma sai kayialwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah zakayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shiba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyua cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya ...

NASIHA AKAN WANDA BAYA SALLAH KO YAKE WASA DA ITA BY MUSA MUHAMMAD MUKTAR

Tsoratarwa Akan Wanda Ba Ya Yin Sallah Ko Yake Wasa Da Ita Tsoratarwa Akan Wanda Ba Ya Yin Sallah Ko Yake Wasa Da Ita Sallah daya ce daga cikin rukunnan musulinci guda biyar wanda musuluncin bawa ba ya cika har ya tsayar da ita. Mazon Allah SAW yana cewa: "Tsakanin mutum da tsakanin shirka da kafirci, shine barin Sallah. (Muslim). Manzon Allah SAW yana cewa: "Alkawarin da yake tsakanin mu da kafurai ita ce sallah, dukkan wanda ya bar sallah to ya kafirta). @ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ ﻭﻏﻴﺮﻩ . Imam Tirmizy ya ruwaito daga Abdillahi bn Shaqeeq al'ukaily yace: "Sahabban Annabi Muhammad s.a.w basu ganin barin aiki wani aiki kafircine inbanda sallah". @ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ. Wato sun hadu akan dukkan wanda ya bar sallah kafiri ne. Manzon Allah s.a.w yana cewa: "Farkon abinda za'ayi wa bawa hisabi akansa na aiyukansa shine sallah, idan ta cika ta yi kyau ya tsira kuma ya rabauta, idan ba ta yi kyau ba kuma bata cika ba ya halaka ya tabe, idan an sami nakasa a cikin f...

029- SUJJADAR RAFKANNUWA (KABALIYYAH DA BA’ADIYYAH) ›

Gabatarwa: Ayanzu da izinin Allah muna son mu kawo bayanaine da suka shafi sujjar rafkannuwa wacce ake kira Kabaliyyah ko ba’adiyya da fatan Allah ya anfanar da mu da wadannan bayanai, kuma ya sanya ya zama sanadiyyar tsira duniya da lahira. Wadannan bayanai za su kunshi me ake nufi da sujjadar rafkannuwa ko mecece kabaliyyah sannan mecece ba’adiyyah, sannan a kawo bayanai na abinda ke sabbaba wadannan sujjadu. Sujjadar Rafkannuwa: Sujjadune guda biyu da mutum yake yinsu bayan ya kammala sallah kafin sallama ko bayan sallama saboda kari ko ragi ko kokwanto da ya yi a cikin sallah. Wannan ta’arifi da ya gabata ya fayyace mana me ake nufi da sujjadar rafkannuwa kuma ya yi bayanin abinda yasa ake yenta da kuma lokacin da ake yenta da kuma dadi nawa ake yi. Kabaliyyah : Sune sujjadu biyu da ake yi bayan tahiyyah kafin sallama, kasancewa ana yinta kafin sallama shi yasa ake kiranta kabaliyyah wato ‘Kabals Salam’. Ba’adiyyah: Sune sujjadu biyu da ake yi bayan an sallame daga sallah, sa...