Skip to main content

031. ABUBUWAN DA SUKE KAWO BA’ADIYYAH (1)

Gabatarwa: Ayanzu za’a kawo bayanaine akan abubuwan da suke sanya ba’adiyyah kadai, da fatan Allah ya an fanar da mu.
Manyan abubuwan da suke haifar da ba’adiyyah, abubuwane kamar haka:
1. Kari (Da mantuwa)
2. Kokwanto
Wadannan sune manyan abubuwan da suke kawo sujjadar ba’adiyyah, kuma akan su za muyi bayani a wannan karon da izinin Allah.
Idan mutum ya yi kari a sallah da rafkannuwa ba wai daganganba to ba’adiyyah zai yi, kamar mutumin da ya kara raka’a a asuba ta zama uku, ko a magariba ta zama hudu, ko kuma a azahar ko la’asar ko kuma lisha ta zama biyar to hukuncinshi anan ya yi sujjadar ba’adiyyah domin ya yi kari.
Haka mutumin da ya kara sujjada a raka’a ta zama uku ko ya kara ruku’i ya zama biyu, amma da mantuwa shi ma ba’adiyyah zai yi.
Wanda ya yi Magana a cikin sallah da mantuwa shima ba’adiyyah zai yi, ko ya sallame daga raka’a biyu da mantuwa, saida ya sallame ya tuna to anan sai ya ciko ragowar raka’o’in sannan ya yi ba’adiyyah.
Wanda ya karanta surori biyu ko sama da biyu a raka’a guda, ko ya fita daga surar da yake karantawa zuwa wata surar ko kuma ya yi ruku’i kafi ya kammala karatun surar duk anan ba komai akan shi, wato ba kabaliyyah kuma ba ba’adiyyah, haka kuma wanda ya yi nuni da hannusa ko da kansa kuma yana cikin sallah, saidai yana rage lada.
Wanda ya maimaita karatun fatiha a raka’a duga da rafkannuwa to shima zai yi ba’adiyyah.
Amma wanda ya tuna cewar bai karanta suraba bayan kuma ya sunkuya zuwa ruku’u to anan bazai koma tsaye domin ya karantaba, saidai bayan sallama ya yi kabaliyyah, saidai idan ya tuna asurtawane ko bayyanawa kafin ya yi ruku’i to anan zai sake karatun, idan karatun surane zai sake karatunne ba wata kabaliyyah ko ba’adiyyah, amma idan karatun fatihane zai sake din amma kuma zai yi ba’adiyyah.
Wanda kuma ya mike bayan ya yi raka’a biyu amma kuma bai zauna ba sai ya tuna kafin hannayansa da gwiwowinsa su bar kasa shikenan sai ya koma ya zauna ba komai akansa, in ko ha ya rabu da kasane to sai ya ci gaba ba zai dawo ya zaunaba saidai zai yi kabaliyyah domin ya rage wani abu a sallarshi, idan kuma bayan ya mikedin ya dawo ya zauna bayan kuma ance da shi ya wuce to anan sallarshi ta yi sai dai zai yi ba’adiyyah ne saboda ya yi kari na wannan mikewar.
Wanda ya yi atishawa a cikin sallah baya cewa ‘’Alhamdu Lillah’’ idan kuma har ya fadadin sallah shi nanan kuma ba komai akanshi, sannan kuma baya maida gaisuwa ga wanda ya gaida shi saboda yana cikin sallah.
Wanda kuma ya yi hamma yana cikin sallah sai ya rufe bakinsa shikenan.
Wanda kuma ya sa wata kalma alokacin da ya karatu wacce ba ta Kur’ani ba zai yi ba’adiyyah ne, amma idan ta Kur’anice babu komai akanshi, saidai idan ya canza lafazi ko ya bata ma’ana to anan sai ya yi ba’adiyyah. Lalle wadannan bayanai za su sa mutsaya mu gyara karatummu na sallah da kuma limamammu, domin ana tafka kurakurai a karatuttukan sallah.
Amma kuma wanda ya manta da ruku’i saida yana sujjadah ya tuna to sai ya koma tsaye, sannan an so ya sake wani abu na karatun sallah, sannan sai ya yi ruku’in ya kuma ci gaba da sallar, bayan ya kammala sai ya yi ba’adiyyah.
Sannan wanda ya manta sujjada guda bai yi ta biyun ba, saida ya mike sannan ya tuna to kawai zai dawo ya zaunane sannan ya yi wannan sujjadar, saidai idan ya yi wannan zaman kafin ya mike to kawai sai ya wuce zuwa gabatar da wannan sujjadar kai-tsaye, bayan ya kammala saii ya yi ba’adiyyah.
Wanda kuma ya manta da sujjadu biyu sai bayan ya mike sannan ya tuna to kawai zai tafi zuwa gabatar da wadannan sujjadunne ba tare da ya zauna ba, sannan ya yi ba’adiyyah.
Kammalawa: Adaidainan zamu dakata kan abinda ya shafi yin ba’adiyyah ta sanadiyyar kari da mantuwa, a karo na gaba bayanai za su zo akan ba’adiyyah ta sanadiyyar kokwanto, da fatan mun anfana.

Post by IRSHAD group of school islamiyya students

1. Musa Muhammad Muktar
2.Mustapha Danjuma
3. Haruna Muhammad
4. Muhammad Auwal
5. Muktar Usman
6. Fadeela Abdulkareem
7. Munira Muhammad
8. Haleemah Umar

Fo  booking call Malama ummi 08065771988completeness

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU. Daga Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano.Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai 'siffatul ijza' (ta wadatar), kuma wacce ake kira 'siffatu kamal' (ta kamala).Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da zaka fara yi shi ne:zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka ، a dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana kayi tsarki kenan، to daga nan kuma sai kayialwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah zakayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shiba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyua cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya ...

NASIHA AKAN WANDA BAYA SALLAH KO YAKE WASA DA ITA BY MUSA MUHAMMAD MUKTAR

Tsoratarwa Akan Wanda Ba Ya Yin Sallah Ko Yake Wasa Da Ita Tsoratarwa Akan Wanda Ba Ya Yin Sallah Ko Yake Wasa Da Ita Sallah daya ce daga cikin rukunnan musulinci guda biyar wanda musuluncin bawa ba ya cika har ya tsayar da ita. Mazon Allah SAW yana cewa: "Tsakanin mutum da tsakanin shirka da kafirci, shine barin Sallah. (Muslim). Manzon Allah SAW yana cewa: "Alkawarin da yake tsakanin mu da kafurai ita ce sallah, dukkan wanda ya bar sallah to ya kafirta). @ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ ﻭﻏﻴﺮﻩ . Imam Tirmizy ya ruwaito daga Abdillahi bn Shaqeeq al'ukaily yace: "Sahabban Annabi Muhammad s.a.w basu ganin barin aiki wani aiki kafircine inbanda sallah". @ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ. Wato sun hadu akan dukkan wanda ya bar sallah kafiri ne. Manzon Allah s.a.w yana cewa: "Farkon abinda za'ayi wa bawa hisabi akansa na aiyukansa shine sallah, idan ta cika ta yi kyau ya tsira kuma ya rabauta, idan ba ta yi kyau ba kuma bata cika ba ya halaka ya tabe, idan an sami nakasa a cikin f...

025- SUNNONIN SALLAH

025- SUNNONIN SALLAH Shinfida: Su sunnonin sallah su ne ke biye da farillan sallah wurin matsayi a cikin sallah, saboda haka kamar yadda bai kamata ka yi wasa da farillan sallah ba to haka yake bai kamata ka yi wasa da sunnonin sallah ba. Wasu da zarar sun ji ance abu kaza sunna ne to basa daukan shi da girma domin suna ganin rashin sa ba zai hana musu sallah ba, alhali kuwa wannan kuskurene mai girman gaske, ai ko ba’a sallah ba duk abinda ka ji an ce sunnane to bai kamata ka yi wasa da shiba. Su wadannan sunnoni na sallah kamar yadda bayani ya gabata matsayinsu baikai na farilla ba domin idan ka bar farilla daya a raka’a sai dai ka ajiye wannan raka’ar ka kawo wata makwafinta kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah a lokacin bayani kan kabaliyyah da ba’adiyya. Kennan su sunnonin sallah ba haka bane, idan mutum ya cika su to sallar shit a cika, idan ko bai cika su ba to sallar shi bata cika ba ko da ko ba zai sake ta ba. Saidai su sunnonin sallah asune ake samun damar kyara...